Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci Jihohin Bauchi da kuma Gombe, a fafautukar neman samun goyon bayan wakilai lokacin zaben fidda gwani a takarar neman wanda jam'iyar APC zata tsayar takarar Shugaban kasa a shekarar 2023.
“Ba a kama kowa ba, amma jami’an tsaro za su ci gaba da yin aiki, har sai sun kamo wadanda suka aikata abin.” In ji shugaban karamar hukumar Ningi Tabla.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na tsakar dare a lokacin da jama'a ke cikin barci.
Dattawan da suka yi fafutukar assasa Jam’iyar PDP, sun gudanar da taro domin shawo kan ka-ce-na-ce dake ci gaba da zafafa a tsakanin ‘ya’yan jam’iyar.
An kammala gasar musabakar karatun Alku'ani ta kasa kashi na 36 da aka kwashe kwanaki tara ana gudanarwa a jihar Bauchi, inda jihar Borno ta zo ta daya a fannin maza, a yayin da kuma a bangaren mata jihar Zamfara ta zo ta farko.
Hukumar samar da agaji kasa da kasa na kasar Amurka USAID, a Jihar Bauchi ta kai ziyara ganewa ido wata cibiyar da mata masu zaman kansu da ke samun horo kan sana’a iri dabam dabam da zai inganta rayuwar matan bayan sun kammala samun kwarewa.
Rahotanni daga hukumomi a Jihar Bauchi na bayanin cewa kwamitin tsaro da suka hada har da jami’an tsaro, suna tsare wasu mutane bisa zargin sayar da katin yin alluran rigakafin coronavirus.
A yayinda Iskar harkokin siyasa ta 2023 ke kadawa a Najeriya, ‘yan kasar sun fara bayyana ra’ayoyinsu kan irin salon siyasa da suke son ganin kasar ta doru a kai.
Bauchi na daya daga cikin jihohin da nau'in cutar mai suna Polio Virus Type 2 ya bulla a yankunan kananan hukumomi 12 a jihar.
Masarautar Bauchi da ta Dass a Najeriya sun bukaci gwamnatin tarayya da kuma ta jihar Bauchi su kafa wani kwamiti da zai binciko matasan da suka ci mutuncinsu a makon da ya gabata.
Rikicin cikin gida a Jam’iyar APC, na kara ta’azzara inda bincike ke bayyana akwai Jihohi sama da goma da rikicin ya shafa.
Al’umomin Unguwar Tirwun da na sashen rukunan Jamiar Abubakar Tafawa Balewa a wajen Birnin Bauchi, sun gudanar da zanga zanga da kuma datse babbar hanyar data wuce Maiduguri,a wani mataki na kin amincewa da assasa Kamfanin tara iskar gas da Kamfanin mai suna Action Energy ke yunkurin ginawa.
Gwamnatin Jihar Bauchi zata dauki karin ma'aikatan kiwon lafiya, tare kuma da inganta rayuwar wadanda ke cikin aikin.
Mai martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu ya sauke wasu masu sarauta su hudu daga kan karagar mulki sabili da hannun da suke dashi wajen taimakawa yan ta’adda da kuma basu mafaka a dazuzzukan Lame.
Bincike na nuni da cewar a Jihar Bauchi ana samun karuwar ayyukan cin zarafin mata musamman fyade wanda a kowacce rana ana samun rahotanni akalla biyar a cewar babban magatakardan manyan kotunan Jihar Bauchi Barrister Emmanuel Sublim.
A ranar Talata Majalisar da ke kula da al’amuran addinin Islama a Najeriya ta NSCIA, wacce ke karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Saa’d Abubakar, ta ayyana cewa za a yi Sallah ne a ranar Alhamis 13 ga watan Mayun 2021.
Shirin agaza ma wasu jihohi a Najeriya da gwamnatin Amurka ta bullo da shi zai taimaka kwarai.
Tawagar ma’aikatan Gidan Radiyon Muryar Amurka a karkashin Jagorancin Hajiya Medina Dauda, ta kai ziyarar ta’aziyya gidan abokin aikinta, marigayi Alhaji Ibrahim Abdulaziz a garin Yola.
Akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta yi amfani da sojojin haya na kasashen waje domin yakar 'yan ta'addan Boko Haram.
Gwamnatin jihar Gombe, ta kakaba dakor hana fita ta tsawon sa’oi ahirin da hudu (24hrs) a yankin Karamar Hukumar Billiri, daga yau Jumma’a sanadiyar tabarbarewar tsaro bayan da aka fara kone konen wuraren Ibada da gidajen Jama’a da dukiyoyi.
Domin Kari