BAUCHI, NIGERIA - Sai dai tun da farko hukumar ta USAID ta gudanar da taron fadakarwa kan muhimmancin ranar mata na Duniya da kuma jan hankulan hukumomi game da bukatun mata don samun cigaba.
Honorable Maryam Garba Bagel, kwamishinar ma’aikatar wutar lantarki, kimiyya da kuma fasahar a jihar Bauchi, ta yi bayani kan bukatun mata, samun ci gabansu da sauran abubuwan da suka shafesu.
Daga bisani hukumar ta USAID ta ziyarci cibiyar da aka kebe domin koya wa matan sana’a, wanda ke karkashin kulawar hukumar Hisba ta hukumar shari’a ta Jihar Bauchi.
Saurari rahoton Muhammad Abdulwahab cikin sauti: