Duk da kasancewar ziyarar da mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, manufar shine ganawa da 'yan siyasa, yakan kai ziyarar girmamawa ga Iyayen kasa da kuma ziyartan manyan malaman Addini.
A fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dr. Rilwan Sulaiman Adamu, farfesa Yemi Osinbanjo, ya bayyana murna da farin ciki dangane da cigaban da ya gani a jihar Bauchin, ya kuma mika gaisuwar shugaban kasa Muhammdu Buhari ta musamman Sarkin Bauchi, inda yace sama da shekaru bakwai kenan yake mataimakin shugaba Buhari, ya kuma bada tabbacin cewa ya samu gogewa kwarai kan batun tafiyar da harkar gwamnati.
A nasa jawabi, Sarkin Bauchi, Mai Martaba Rilwan Sulaiman Adamu, ya bayyana farin cikinsa da na al’ummar masarautar kan ziyaran da mataimakin shugaban Najeriya ya kawo, yace wannan ya nuna irin muhimmanci da kuma darajar da mataimakin shugaban ke nunawa wa masarautu.
Sarkin Bauchi ya shaida masa cewa masu sarauta ba 'yan siyasa bane. Bisa ga cewarsa, Allah ke bada mulki, kuma a matsayinsu na Iyayen kasa nasu bada shawara ne kawai.
Kafin ya bar jihar Bauchi, Farfesa Yemi Osinbajo, ya kai ziyara gidan, Sheik Tahir Usaman Bauchi, ya kuma ziyarvi kabarin marigayi, Sir Abubakar Tafawa Balewa, Daga bisani ya karkare ziyarar tasa da ganawa da wakilai 'yan jam’iyarsa ta APC.
Tunda farko kuwa Farfesa Yemi Osinbajo, saida ya ziyarci jihar Gombe inda ya gana da gwamna Muhammed Inuwa Yahaya a gidan gwamnati, da kuma ziyartan Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar, a fadarsa.
Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Mohammed cikin sauti: