Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Bauchi Ya Tsige Wasu Sarakuna Hudu Bisa Zargin Taimaka Wa ‘Yan Ta’adda


Mai martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu ya sauke wasu masu sarauta su hudu daga kan karagar mulki sabili da hannun da suke dashi wajen taimakawa yan ta’adda da kuma basu mafaka a dazuzzukan Lame.

Masu sarautan da aka warware wa rawunnan sun fito ne daga garuruwan Buruku, Turkunyan Biru, Gamawa da kuma Zomo dukkaninsu a masarautar Lame da ke Karamar Hukumar Toro, a Jihar Bauchi.

Sarkin Yakin Bauchi, Alhaji Aliyu Yakubu Lame ya fayyace dalilan da yasa mai Mai martaba Sarkin Bauchi, Dokta Rilwan Suleiman Adamu daukan wannan mataki na cire masu sarautun, inda yace an tube sarautan ne sabili da yadda bakin haure ke shigowa daga Zamfara, su yanka masu fili su zauna bayan an basu kudi, shi ya sa aka yi shawara a tube su. Ya kara da cewa har sukan ma yi anfani da dillalai wajen cinikin.

A gefe guda kuma, Muryar Amurka ta tuntubi kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Bauchi, Alhaji Nuhu Zaki, inda shi kuma ya ce gwamnati ba za ta lamunci irin wannan halayya ba kuma za a hukunta duk wanda aka same shi da hannun ciki.

Al’ummomin garuruwan Buruku, da Turkunyan Biru, da na Gamawa da kuma Zomo da su ke karkashin hakimin Lame a jihar Bauchi sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da lamarin.

A yayin da wasu ke ganin hukuncin da aka dauka na cire masu sarautan daga kan mukamansu bai dace ba sabili da an yi hanzari wajen aiwatar da hukuncin, wasu ko cewa su ka yi ya dace, domin a tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.

Muryar Amurka ta tuntubi Kwamishina mai kula da Kananan hukumomi na jihar Bauchi, Honorabul Nuhu Zaki domin sanin ko akwai matakai da aka dauka a hukumance. Ya kuma ce tun lokacin da aka yi ta samun bayanai dabban dabban ne ya sa sojoji, ‘yan sanda, da ‘yan banga suka far masu a wadannan dazukan, sai aka samu saukin lamarin.

Shi kuwa honorabul Mahmud Hassan Tabla, wanda shi ne shugaban Karamar Hukumar Ningi, wanda dajin Burra ke karkashinsa, cewa yayi bayan bayanan da aka samu na miyagun mutanen ne yasa gwaman ya tura sojoji cikin motoci akalla 100 da jiragen sama zuwa dazukan inda suka rutsa da su, suna ta lugudan wuta. Tun daga nan aka samu sauki.

XS
SM
MD
LG