Sannan Cibiyar bunkasa binciken fasahar zamani a cikin al’umma wanda ake kira da CITAD, a takaice ta ce ta gano dalilan da wasu jihohi a Arewacin Najeriya suke kin amincewa da karban allurar rigakafin COVID-19.
A jawabinsa ga taron manema labarai a ofishinsa, kodinetan shirin, Mallam Hamza Ibrahim ya bukaci ganin hukumomin ayyukan lafiyan na wadannan jihohi guda shida da su tashi haikan wajen shawo kan matsalolin da suke kawo tangarda ga shirin alluran COVID-19 din.
Ya ce ana wayar da kan mutane saboda su gane muhimmancin allurar da kuma su san ce wa allurar bata hana haihuwa su kuma daina jin labaran bogi.
A halin da ake ciki kuma, jami’ar wayar da kan al’umma a cibiyar bunkasa bincikenfasahar zamani a cikin al’umma, CITAD, Hajiya Halima tayi karin haske kan batun mutane biyar din da ake tsare dasu kan zargin sayar da katin shaidar Alluran rigakafin COVID-19.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Abdulwahab: