A jawabinsa na bayyana godiya game da yadda musabakar ta gudana, Gwamnan Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammed Kauran Bauchi, ya ce kwanaki tara da aka yi ana fafatawa a musabakar tsakanin matasa maza da mata, daga jihohi 36 da kuma Abuja, kowanne ya nuna kokarinsa a fannin da ya yi takarar akai,
Gwamnan na Bauchi ya yabawa alkalai da suka yi alakalanci a musabakar, kuma ya ce sun gudanar da hukunci da ya dace wanda kowa ya yi na’am da shi kana aka yaba da shi.
A jawabinsa na rufe musabakar, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, shima ya yabawa Gwamnan jihar Bauchi da uwargidansa sabili da daukar nauyin gudanar da musabakar inda ya yi addu’ar Allah Ya saka da Aljannatul Firdaus.
An dai fara gudanar da musabakar karatun Alkur’ani a Najeriya a shekarar 1986 a karkashin jami’ar Usman Danfodio dake Sakkwato. Wadanda zasu zo na farko a bangaren maza da mata sune zasu wakilci kasar Najeriya a musabakar duniya da za a gudanar a kasar Saudi Arabiya.
Ga rahoton Abdulwahab Mohammed cikin sauti: