Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin PDP Sun Gudanar Da Taron Neman Hadin Kai


Wasu daga cikin shugabannin jam'iyyar PDP
Wasu daga cikin shugabannin jam'iyyar PDP

Dattawan da suka yi fafutukar assasa Jam’iyar PDP, sun gudanar da taro domin shawo kan ka-ce-na-ce dake ci gaba da zafafa a tsakanin ‘ya’yan jam’iyar.

Hakan ya biyo bayan ayyana sunayen mutane biyu da kwamitin Farfesa Ango Abdulahi, kuma shugaban kungiyar dattawan Arewa ya gudana a garin Minna na Jihar Neja, da aka ce gwamnan Bauchi, Senata Bala Abdulkadir Muhammed da kuma tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Senata Bukola Saraki.

Kamar yadda bincike ya nuna mutane hudu masu son yin takarar kujerar shugabancin kasa a jam’iyar PDP da suka hada da, gwaman Sokoto, Aminu Tambuwal, da Alhaji Aminu Hayatu-Deen, da Bala Abdulkadir Muhammed, gwamnan Bauchi, da kuma Senata Bukola Saraki sun amince da fidda dan taka guda daga cikinsu, amma da sakamako ya fito sai aka samu canjin ra’ayi.

Dokta Ladan Salihu, dan jam’iyar PDP ne kuma ya halarci wajen taron da aka gudanar a garin Minna, yayi fashin baki kan batun jeka ka dawo da ake yi. Ya ce ya kamata su samu hadin kai.

Mallam Dogo B B, shi ya jagoranci zaman taron Dattawan Jam’iyar PDP din da aka gudanar a Bauchi ya bukaci ganin uwar jam’iyar PDP din data gayyaci duk ‘yan takaran don neman maslaha.

Madam Hauwa Aliyu, daga jihar Yobe, ta amince da sakamakon kwamitin farfesa Ango Abdullahi, sai dai tana goyon bayan takarar, wamnan Bauchi Senata Bala Abdulkadir Muhammed Kauran Bauchi.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Abdulwahab:

Shugabannin PDP Sun Gudanar Da Wani Taron Neman Hadin Kai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG