An gudanar da taron kaddamar da shirin hukumar USAID ta kasar Amurka mai tallafa wa kasashe, wanda wannan shirin zai mai da hankali ne kan batun tantance ayyuka, fayyace su da kuma tabbatar da ingncinsu a fannoni daban-daban a wasu zababbun jihohin Najeriya.
Jihohin da za su amfana daga shirin sun hada da Adamawa, Akwai Ibom, Bauchi, Ebonyi, Gombe da kuma Sokoto.
An yi da taron ne a kebabben wurin gudanarwa na jihar Bauchi. Gwamnonin jihohi guda shida da za su amfana da shirin sun gabatar da jawabansu ta akwatin talabijin.
Har ila yau wakilan hukumomin gwamnatoci da kuma jakadar kasar Amurka a Najeriya Mary Berth, da kuma Ministan Kudin Najeriya, sun gabatar da jawabai ta hanyar da aka haska su ta akwatinan telebijin da ake gani kai tsaye.
A bayan kammala taron, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir, ya ce gwamnan jihar Bauchi, ta na maraba da wannan shirin, da kuma fatan zai taimaka wajen ciyar da jihohin gaba, da tabbatar da cewa ana amfani da kudaden al'umma yadda ya kamata.
Domin karin bayani sai a saurari rahoton Abdulwahab Muhammad a cikin sauti.