Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siyasar Karba-Karba Ya Kawo Nakasa a Tsarin Mulkin Demokradiya: Shekh Yahaya


A yayinda Iskar harkokin siyasa ta 2023 ke kadawa a Najeriya, ‘yan kasar sun fara bayyana ra’ayoyinsu kan irin salon siyasa da suke son ganin kasar ta doru a kai.

A taron wa’azi na kasa da kasa daya gudana a Bauchi, shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’ah, (JIBWIS), Sheik Muhammadu Sani Yahaya Jingir, ya bayyana cewa tsarin siyasar karba-karba ya kawo nakasu wa tsarin mulki irin ta Dimokaradiya.

Shugaban Majalisar Malaman, Sheik Muhammadu Sani Yahaya Jingir, yayi wannan furuci ne a hira da manema labarai a karshen taron wa’azin

Da aka tambayeshi game da batun tsaro a Najeriya, shugaban na Majalisar ta Malamai, ya danganta faruwan hakan kan kasashen ketare, da kuma wasu kabilu da basu son zaman lafiya a Najeriya.

Daga bisani Malamin, yayi addu’ar zaman lafiya a Najeriya da kuma baiwa shugabanni ikon gudanar da mulki mai adalci.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Abdulwahab:

Tsarin Siyasar Karba-Karba Ya Kawo Nakasa Wa Tsarin Mulkin Demokradiya: Shekh Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG