Wasu mayaka sun farma wani gidan gajiyayyu a Yemen

Gidajen gajiyayyu da wasu mayaka suka farma a Yemen jami'an tsaro sun kewayeshi bayan harin

Hukumomi a Yemen sun ce wasu mayakan sa-kai da suka far ma wani gidan gajiyayyu a Aden sun kashe akalla mutane 15 ciki har da wasu matan kiristoci da ke gudanar da ayyukan jin kai, wadanda suka fito daga India.

Jami’an tsaron sun ce maharan sun shiga gidan ne da muggan makamai, inda suka bude wuta akan mutane.

Wata majiya ta ce, maharan sun fara kashe matan da ke ayyukan jin kan ne a lokaci da suka shiga ginin, sannan daga baya suka daure gajiyyun da ke cikin ginin suka kuma harbe su.

Kafofin yada labaran kasar ta Yemen da likitocin kungiyar Docors without borders, sun ruwaito cewa baya ga matan Indian su hudu da aka kashe, maharan sun kuma harbe wasu matan Yemen su biyu da ke aiki a wurin da kuma gajiyayyu takwas da wani mai gadin ginin.

Shi dai wannan gini yana Gundumar Sheikh Osman ne a birnin na Aden.

Ya zuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin wannan hari, sai dai a baya-bayan nan, ana alakanta ‘yan kungiyar IS da wasu hare-hare da ake kaiwa a birnin na Aden.