Jagoran tattaunawar a garin Geneva daga Majalisar Dinkin Duniya Ould Cheikh Ahmed ya bayyana matukar damuwa game da ci gaba da yaki tsakanin sojoji masu goyon bayan gwamnati da ‘yan tawayen Houthi.
Jami’an tsaron Yemen sun ce akalla mutane 68 aka kashe a ‘yan tsakanin kwanakin nan a lardin Hajjahh kusa da kan iyakar kasar Yemen da Saudiyya. Matattun sun hada da ‘yan Houthi guda 40 da sojojin gwamnati guda 28.
Sai kuma wadanda suka jikkata daga dukkan bangarorin biyu masu fada da juna, wadanda a jiya Asabar suka yarda da kafa kwamitin da zai kalli maganar tsagaita wuta a Tsakani.
Majalisar Dinkin Duniya tace fiye da mutane 5,800 yakin ya lakume daga bara zuwa bana.