Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Amurka Ya Hallaka Mataimakin Shugaban al-Qaida Na Yemen


Mabuyar 'yan al-Qaida a Yemen da aka kaiwa hari
Mabuyar 'yan al-Qaida a Yemen da aka kaiwa hari

Kungiyar al-Qaida a Yemen ta tabbatar da mutuwar mataimakin shugabanta a wani hari da Amurka ta kai da jirgin sama mai sarafa kansa da kansa

Kungiyar al-Qaida ta fada yau Talata cewa an kashe Nasir al-Wuhayshi, mataimakin shugaban kungiyarsu dake reshen Yemen a wani hari da jirgin Amurka mara matuki ya kai cikin makon da ya gabata.

A wata sanarwa ta faifan bidiyo, kungiyar ta fadi cewa farmakin da aka kai a kudu maso gabashin birnin Mukalla ya kashe Wuhayshi, da wasu su biyu. Kungiyar kuma ta nada Qassim al-Rimi a matsayin sabon shugaban ta na kungiyar dake mashigin yankin na larabawa da ake kira AQAP a takaice.

Jami’an Amurka sun fada a maraicen jiya Litinin cewa suna kan aiki wajen tabbatar da mutuwar Wuhayshi, amma basu fadi ko ‘yan hukumar leken asirin kasar ta Amurka ne su suka kai harin ba.

Wuhayshi shi ne mataimakin shugaban kungiyar al-Qaida Ayman al-Zawarihi, ya kuma taba zama dan aiken tsohon shugaban kungiyar Osama Bin Laden. Ya zamo shugaban kungiyar ta AQAP, rashen da Amurka ta dauka a matsayin kungiyar al-Qaida mafi muni a shekarar 2009.

A karkashin jagorancin Wuhaishi, kungiyar ta AQAP ta gudanar da wasu gagaruman shirye-shirye, ciki har da yunkurin kai ma wani jirgin sama na Amurka hari ranar Krisimati. A watan Janairu kuma, kungiyar ta dauki alhakin kai mummnan hari a ofisoshin mujallar barkwanchin Cherlie Hebdo dake Paris.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG