Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yanzu haka yana kasar Saudiya ya kuma ce zai yi magana kan kudurin tsagaita wuta na jinkai a yakin da Saudi ke jagorantar kai hare-hare kan ‘yan tawayen Houthi dake kasar Yemen.
John Kerry yace, “muna kira ga duk ‘bangarorin biyu, duk wanda ke da hannu su mutuntadokar jin kai, da kuma ‘daukar duk hanyoyin da suka kamata na tabbatar da an kare farar hula daga fada da ake yi, a kuma bayar da damar shigar da kayan agaji ga masu bukata.”
Kerry zai hadu da shugabannin kasar Saudiya da Abdu Rabu Mansour Hadi shugaban kasar Yemen, wanda yayi gudun hijira zuwa Saudiya.
Kasar Saudiyar dai ta ce tana nazarindakatar da kai hare haren ta sama dama sauran matakan data ke ‘dauka kan ‘yan tawayen na Houthi. Ma’aikatan jin kai na kuka kan wahalar shigar da abinci da sauran kayan bukatu ga fararen hular kasar Yemen.
Kerry dai yace dakatarwar da za’ayi dole ne ayi ta hanyar da bazata baiwa kowa damar ‘kara kame wani yanki ba, ko kai hari ga wanda suka ajiye makamansu.
Alokacin da ya ziyarci kasar Jibuti dake kur’yar Africa ranar Laraba, Kerry ya bayyana wani sabon gudummawar dala milyan 68 da Amurka zata baiwa kasar Yemen. Taimakon dai zai hada da kudin ga hukumomin da suke samar da ci- maka, da ruwan sha da mafaka, dama sauran wasu bukatu ga ‘yan kasar Yemen wadanda suke da bukata.