Wani babban jami’in gwamnati ne ya tabbatar da aukuwar wannan lamari.
A jiya Talati Shugaba Hadi ya ce zai sauya ministoci da dama, ciki har da ministan harkokin wajen kasar, Riyad Yassin.
Majiyar ta gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, shugaba Hadi ya yi shirin gudanar da garambawul din ne, ba tare da tuntubar Firayim Minista Bahah ba, wanda har ila yau shi ne mataimakin shugaban kasar.
A watan da ya gabata, shugaba Hadi da ke samun goyon bayan kasar Saudiya, ya koma birnin Aden, bayan da ‘yan tawayen Houthi da Iran ke marawa baya suka sa ya yi kaurar dole a watan Maris.
Ana dai kallon wannan mataki na Hadi a matsayin yunkurin sake assasa ikonsa, bayan da magoya bayansa suka sake karbe ikon yankunan da mayakan Houthi suka mallake a baya.