Harin ya hallakka akalla mutane 31 ya kuma raunata kusan mutane 20. ‘Yan ta’addar sun ce harin daukar fansa ne akan ‘yan tawayen shi’ar HOUTHI da Iran ke marawa baya suka kuma cika babban birnin.
Su dai ‘yan tsaurin ra’ayin Islamar ISIS mabiya darikar Sunni ne da suke kallo ‘yan Shi’a a matsayin fandararru.
Harin dai ya kuduri masallatan ‘yan Houthi ne da ofisohinsu. Bam din masallacin ya tashi ne a lokacin da masu ibada ke shirin fara azumin wata mai tsarki na Ramadan.
‘Yan Houthin dai sun warce ikon babban birnin ne a bara wanda hakan ya tursasawa mai mulkin kasar ABD-RABU MANSOUR HADI rugawa zuwa kasar Saudi Arabia.
Tun lokacin Saudin ke ruwan wuta ta sama da kasa ga ‘yan Houthi, su kuma MDD sun shirya taron sulhun da har yanzu ya ci tura.