An fara tattaunawar neman sulhu tsakanin kungiyoyin mayakan Yemen da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta, a lokacin da Saudi ke cigaba da jagorantar kai hare hare ta jiragen sama akan ‘yan tawayen Houthi a babban birnin sana’a.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yayi kira ga mayakan gwamnati da mayakan ‘yan tawaye da su tsagaita wuta don bada taimakon jinkai ta akalla tsawon makonni biyu, kasancewar za’a fara Azumin watan Ramadan, watan da ya kamata ya zamanto lokacin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ban Ki-moon yayi wannan furuci ne a birnin Ganeva, inda wakilin sa ke kokarin gabatar da wasu tarurruka da wakilan gwamnatin shugaba Abd Rabbu Mansour Hadi, da ‘yan tawayen Houthi wanda ke rike da babban birnin Yeman.
Wannan zaman sulhun shine mataki na farko da aka dauka tun barkewar fadan watanni uku da suka wuce, amma zaman da za’ayi babu tabbacin za’a yishi ne gaba da gaba.
Ministan harkokin wajen Yemen Reyad Yassin Abdulla yace gwamnatin sa zata fara tattaunawa kan batun tsagaita wuta da ‘yan tawayen Houthi, amma sai in har sun fice daga biranen da suka mamaye, sun kuma saki dubunnan mutanen da suka kame da kuma yarda da kudurin da Majalisar Dinkin Duniya ta shinfida.