Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Yemen ta Bada Sharadin Halartar Taron Sulhu


Shugaban Yemen Abdu Rabu Mansour Hadi, shi da gwamnatinsa na Saudiya
Shugaban Yemen Abdu Rabu Mansour Hadi, shi da gwamnatinsa na Saudiya

Gwamnatin Yemen dake gudun hijira ba zata halarci taron sulhu da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya sai dai 'yan tawayen Houthi sun janye daga wuraren da suka cafke

Shugaban gwamnatin Yemen dake gudun hijira Abdu Rabu Mansour Hadi a baya can ya tabbatar gwamnatinsa zata halarci taron zaman lafiya da za'a yi wannan makon a Oman tsakanin gwamnatinsa da 'yan tawayen Houthi.

Amma jiya Lahadi a wata sanarwa da gwamnatin ta fitar tace sun yanke shawara ba zasu halarci taron da Majalisar Dinkin Duniya take shirya wa ba sai 'yan tawayen Houthi sun amince da kuduri mai lamba 2216 kuma su yadda su yi aiki da shi ba tare da gindiya wasu sharuda ba.

Sanarwar ta biyo bayan rashin samun bangarorin biyu su zauna kan teburin shawara saboda samo bakin zaren rikicin da ya addabi kasar Larabawar da ta fi kowacce talauci a duniya.

Shugaba Hadi ya arce ne daga Yemen tare da gwamnatinsa farkon wannan shekarar. Yanzu suna kasar Saudiya daga inda suke gudanar da ayyukansu.

Tun watan Satumbar bara da 'yan tawayen Houthi suka shiga Sana'a babban birnin kasar kungiyoyi da dama suke ta fafatawa da juna kowannensu yana neman kama madafin ikon kasar. Fadace fadacen sun yi sanadiyar mutuwar mayaka da fararen hula fiye da 4,500.

Duk kasashen Larabawa dake yankin gulf ban da Oman sun hada hannun da Saudiya wajen yaki da 'yan tawayen Houthi dake samun gyon bayan kasar Iran.

Cikin 'yan makonnin nan dakarun dake goyon bayan gwamnatin kasar sun soma samun galaba akan 'yan tawayen tare da sake cafke wasu wuraren da suka mamaye da. Jiya Lahadi ma dakarun dake biyayya ga Shugaba Hadi sun kaddamar da wani gagarumin farmaki kan 'yan tawayen a gabashin birnin Sana'a

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG