Kawo yanzu kwamitin ya tantace mutane 68 daga jihar Kaduna da mutane 48 daga jihar Katsina da mutane 11 daga jihar Jigawa da mutane uku daga jihar Bauchi da mutum daya daga Sokoto da 10 daga Zamfara da hudu daga jihar Neja da biyu daga Adamawa da daya daga jihar Filato,
Duk wadanda aka lissafa kwamitin yace ya tantancesu amma saboda gujewa cakudewa sun dauki rabon hawa biyu saboda sun tantance 'yan jihar Kano mutane 103. 'Yan kwamitin na kyautata zaton shanun 'yan Kanon suna cikin wadanda aka gano yanzu da suke hannunsu.
Onarebul Murtala Sulengaro shugaban kwamitin ya bayyana adadin shanun da jami'an tsaro suka danka masu. An basu a rubuce adadin dabbobi 818 sai kuma wasu 218 da suka kara samowa daga barayi kwanaki biyu da suka gabata.
Sace shanu daga Fulani makiyaya a yankin arewa wani abu sabo ne da ya kunno kai dalili ke nan gwamnan Kano Dr Ganduje yace gwamnonin arewa na hada karfi da karfe su yaki wannan sabuwar annobar.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5