Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

LEGAS: Miyetti Allah ta Gano Shanun Sata


Fulani makiyaya
Fulani makiyaya

A taron manema labarai da shugabannin kungiyar Fulani ta Miyrtti Allah suka kira a birnin Legas sun bayyana gano wasu shanun sata.

Inji kungiyar daga farkon watan wannan shekarar zuwa yanzu sun kama shanu fiye da dari da aka sata daga Fulani.

Barayin shanun ko wakilansu sun yi kokarin sayar dasu a babbar kasuwar dabbobi dake Legas. Alhaji Abdullahi Laliga shugaban kungiyar Miyetti Allah a babbar mayankar dabbobi da ake fitowa dasu daga yankin arewacin Najeriya yace suna da shanu ashirin da uku a hannunsu da suka kama. Yace wasu sun gaya masu cewa wani soja da dagaji da hakimi ne suka sayar masu. Su ukun an dankasu a hannun hukuma. Mutanen sun fada da bakinsu cewa shanun na sata ne.

Shanun an satosu ne daga Kaduna. Shugabn yace su basu ga wani canji ba sai kashe Fulani da ake yi da sace dukiyoyinsu.

Har wayau shugabannin Fulani a Najeriya sun koka gameda abun da suka kira neman kassara Fulani da sana'ar da aka sansu da ita kaka da kakanni bisa ga la'akari da yawan satan shanu da ya addabesu ba tare da gwamnati tayi wani abu ko karesu ba.

Alhaji Bello Dan Magwaffa Sarkin Fulanin babbar mayakan jihar Legas yace yana ganin matsalolin da Fulani suka shiga Allah kadai ya san iyakarsu. Yace ana kore shanu dubu daya ko dubu biyu da bindigogi har ma wasu Fulanin a kashesu. Wasu ma dauresu ake yi kana a ce sai sun bayar da nera miliyan biyu ko uku. Ya kira gwamnati ta shiga lamarin domin kada su Fulanin su shiga daji su hada kai da 'yan ta'ada.

Kungiyar ta Miyetti Allah ta mika mutane biyar ga 'yansanda domin cigaba da gudanar da bincike game da shanun satan da aka samesu dashi. Kungiyar ta gayyaci makiyaya daga Kaduna da Zamfara da aka sace shanunsu da su ziyarci Legas domin tantance shanunsu.

Ga rahoton Babangida Jibril.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00
Shiga Kai Tsaye


.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG