Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Shiroro Honorabul Abdullahi Yarima y ace kwanan baya barayin sun sace wata yarinya a kauyen Gurmuna da kyar ta kubuce ta dawo kuma kwanan nan sun kashe wani yaro mai suna Danladi Sabonkudi a Basa. Y ace kwanan nan ma sun shiga kasar ta Basa su ka sace shanu garke biyu na wani Bafullace mai suna Dandare. Honorabul Yarima ya roki gwamnati da ta dau matakin da ya dace cikin lokaci.
Wakilinmu a jihar Naija wanda ya turo mana da wannan rahoton Mustapha Nasiru Batsari, y ace hatta Majalisar Dokokin Jahar ta kira Kwamishinan ‘Yansanda jahar don sanin matakan da rundunarsa ke daukawa a kan wannan al’amarin. Mustapha ya ruwaito Danmajalisar Dokokin Karamar Hukumar Rafi, inda nan abin ya fi muni, Alhaji Muhammad Danlami Bako na cewa saboda damunsu da abin ya yi ne ma su ka kira Kwamishinan ‘Yansandan Jahar, kuma su na bukatar gwamnati ta dau mataki musamman ganin yadda ake bai wa rundunar ‘yansandan kudi kadan.
To saidai kuma duk da zargin rashin samun kwarin gwiwa daga gwamnati, rundunar ‘yansandan jahar, in ji Mustapha, ta ce ta tabuka saboda ta damke wasu daga cikin miyagun. Kakakin rundunar Mr. Bala Elkana y ace ko kwanan nan ma sun damke 30 daga cikinsu, banda shanun da su ka sake kwato, wanda ko kwanan baya ma sun kwato 600.