Shugaban kungiyar Miyetti Allah na Jihar Lagos, kuma daya daga cikin shugabannin kasuwar, Alhaji Abdullahi La Liga, ya shaidawa Muryar Amurka cewa sun gano wadannan shanun na sata ne saboda dukkansu mata ne matasa, in banda wani dan su guda daya. Yace babu wani makiyayin da zai debi shanun da suka fara haihuwa, ya saida su.
Alhaji Abdullahi La Liga ya ci gaba da cewa, shanun kasuwa dabam suke, kuma da zarar an shigo da shanu idan har bana kasuwa bane zasu gane.
Ya kara da cewa sun kai rahoto da kuma kuka ga hukuma, amma ba su ga alamar ana yin wani abu a kai ba. Don haka ne suka nemi 'yan jarida domin idan wadanda aka sace musu shanu sun ji, su biyo sawu.
Sarkin Fulanin babbar kasuwar shanun, Alhaji Buba Hamma Baffa, yace akwai gazawar hukuma a wuraren da ake zuba wadannan shanu a cikin ababen hawa, domin basu bincike suba, kuma basu tabbatar da asalinsu kafin a kama hanya da su ba.
Shugaban mahauta na wannan kasuwa, Alhaji Umar Adam, yace ba wannan ne karon farko da ake kawo shanun sata ba.
Ana sauke shanu kimanin motocin tirela 25 kowace rana a wannan kasuwar shanu dake Oko-Oba a Lagos. Sannan kuma, ana yanka shanu dubu daya da dari biyu kullum.
Shugabannin kasuwar dai suka ce mutumin da yayi ikirarin cewa shanunsa ne aka kawo kasuwar daga arewa, yayi magana da su ta waya amma har yanzu ba su gan shi ba.