Gwamna Muazu Babangida Aliyu na jihar Neja kuma shugaban gwamnonin arewa yace wasu batagari ne suke haddasa rigima tsakanin makiyaya da manoma. Gwamnan yace gwamnonin sun saurari korafin makiyayan kuma za'a dauki matakan shawo kan matsalolin.
Yace nan da shekara daya duk inda layukan shanu suke da suke bi to za'a yi kokari a dawo dasu. Yace dole ne a taimakawa makiyaya domin a samu madara da ta wadata. Yayi misali da saniyar Afirka Ta Kudu wadda zata iya ba mutum madara bokiti biyu rana guda amma ta Najeriya da kyar ta ba mutum kwano biyu na awo. Domin haka dole a hadasu domin ingantawa.
Shugaban Miyatti Allah na kasa Mohammadu Curwa Ardon Zuru yace suna son su ga menene gwamnonin zasu yi domin su san abubuwan da zasu yi. Shi ma wani shugaban Fulani ya wanke al'ummarsa daga tada fitina. Yace wasu mutane ne da suka shigo cikin alamura na Fulani suna bata masu suna.
Mukaddashin gwamnan jihar Taraba yace za'a aiwatar da duk kudurorin da aka cimma. Yace sun samu ainihin hanyoyin da suke bi suna wucewa. Dama kwamisahanan aikin gona na jiharsa ya fara dubawa kafin taron. Yanzu zasu koma su fitar da hanyoyin. Zasu ingantasu domin makiyayansu su zauna waje guda.
Ga karin bayani.