'Yan bindigan sun hada shanun tare da wani mutum wanda kawo yanzu ba'a san inda yake ba. Amma a wannan karon 'yan bindigan basu kashe kowa ba. Sun fadawa mutanen kauyen cewa ba kisa suka zo yi ba illa dai sun zo neman abinci da kayan masarufi. Sabili da haka suka tafi da shanun da yawansu ya fi dari.
Wani mazaunin kauyen yace sun zo da bindigogi kuma suna fadawa mutane su kwantar da hankalinsu domin abinci suka zo nema. Sun dauki mai kiwon sun tilasta masa ya rakasu. Lokacin da abun ya faru mutanen garin sun gudu amma da alama yanzu sun soma dawowa. Bisa ga duk alamu babu jami'an tsaro a kauyen duk da yana gaf da dajin Sambisa.
Shugaban karamar hukumar Madagali Mr. Watanda ya tabbatar da harin na 'yan bindigan. Yace sun tafi da shanu ta hanyar Damboa kuma kowa yana tsoro.
A jihar Taraba kuma wasu 'yan bindiga sun farma kauyen Tunari dake yankin Wukari, wurin dake fama da harin sari ka noke. Wasu da suka yi magana sun ce an kashe mutane tare da kone gidaje. Wasu kuma sun shiga daji kuma ba'a san inda suke ba.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz