Kungiyar Fulanin ta dora alhakin satar dabbobi da satar Fulanin kansu akan Fulani.
Amma kungiyar ta nemi sabuwar gwamnati mai shigowa ta yiwa Allah ta shawo kan lamarin. Mataimakin kungiyar na kasa Alhaji Husseini Boso ya bayyana hakan. Yace hukuma ita ce da hakin kare kowa.Su a kungiyance suna wayar da kawunan 'yanuwansu tare da kira garesu su bar wannan muguwar dabi'a da wasu cikinsu suka shiga. Yace abun takaici yanzu shi ne wasu sai su sace mata da 'ya'yansu kana su sami maigida ya biya kudin fansa. Shi kuma maigidan dole ya kwashi shanu ashirin ko talatin ya sayar saboda ya biya kudin fansa.
Alhaji Boso yace shugabansu na yankin jihar Kogi sun saceshi kusan shekara daya ke nan. Sun karbi kudi daga wurin iyalansa amma har yanzu babu duriyarsa. Basu sakoshi ba, kuma ba'a gane inda yake ba. Sun sanarda hukuma amma babu abun da aka yi. Yace idan aka yi sakaci matsalar Fulani zata zo ta fi ta Boko Haram a Najeriya.
A cigaba da yin bayani Alhaji Boso ya furta ra'ayinsu akan matakan da gwamnatin Ghana ta dauka akan Fulani na korar wasunsu daga kasar suna cewa Fulanin ba 'yan kasa ba ne. Yace sun rubutawa gwamnatin Najeriya akan lamarin domin Fulanin Ghana 'yan kasa ne kamar sauran kabilun kasar suke.Yace a saninsa idan mutum ya yi laifi hukuntashi ake yi ba wai a koreshi ba.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.