Bayanai na nuna cewa taron dangin da gwamnatocin jahohin arewacin Najeriya biyar su ka yi ma barayin shanu ya fara haifar da da mai ido.
Wakilinmu a Minna Mustapha Nasiru Batsari ya lura cewa kwanan baya ne gwamnonin na jahohin Kaduna da Katsina da Naija da Zamfara da Kebbi da Naija su ka kafa wani shiri na far ma barayin shanun da su ka buya a dajin Kamuku da ke jahar Kaduna. Tun sannan an yi ta samun nasarar fatattakar barayin shanun kuma har Fulani makiyaya sun ce sun fara ganin haka zahiri.
Mataimakin Shugaban Kungiyar Fulani Makiyayi ta Miyatti Allah, shiyyar jahar Naija Alhaji Muhammadu Shehu y ace babu abin da za su ce sai godiya ga Allah saboda rabon a samu korafin bacewar shanu an dank wan biyu. To amma ya yi kira ga gwamnatocin jahohin biyar da kar su yi sanyi, a maimakon haka ma su kara azama. Y ace lallai su na masu gamsuwa da jajircewar da gwamnonin su ka yi.
A halin da ake ciki kuma, wasu malamai sun shiga addu’o’i da bayar da shawarwari game da batun samar da zaman lafiya a Najeriya da kuma tsugunar da yara kana da ke gararanba bisa kan tituna saboda dalilai daban-daban.