Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Kwato Shanun Sata Ya Soma Samun Nasara


Shanun
Shanun

Kwamitin da shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya kafa watan jiya saboda yaki da masu satar shanu ya soma samun nasara.

Kwamitin da shugaba Buhari ya kafa saboda yakar masu satar shanu a jihohi biyar ya soma cimma nasara.

Kwamitin tare da hadin gwiwar hukumomin kasar Nijar sun kwato shanu 503 da awaki 25 da tumaki sama da 190 da barayi suka sace daga jihar Katsina ta arewacin Najeriya.

A jihar Kaduna kuwa kwamitin ya kama shanu 2,000 wadanda yanzu ana cigiyar masu shanun.

Sakataren kungiyar makiyaya ta kasa wato Miyetti Allah Alhaji Baba Usman Gelzama ya tabbatar da kama shanun. Yace kwamitin da shugaba Buhari ya kafa ya kama hanyar warware matsalar da ta addabi al'ummar Fulani.

To amma a jihar Taraba Fulani sun koka da karuwar sace-sacen shanu a yankin.Ko kwanaki biyu da suka wuce kimanin shanu 400 wasu barayi da ake kyautata zato sun tsallako ne daga jihar Filato suka sace a kananan hulumomin Wukari da Ibi.

Alhaji Mafindi Umaru Dan Buram tsohon shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Taraba ya nuna takaicinsa dangane da uwar kungiya ta kasa ke gudanar da harkokinta. Haka ma dan Buram ya soki yadda kungiyar ta soke kwamiti din jihohi lamarin da yace ya dagula kokarin kawar da satar shanu.

To saidai a yankin Ibi barayin shanun sun canza salon yadda suke sata yanzu

Ga rahoton Sanusi Adamu

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG