Sai dai kawo yanzu kanfanin dillacin labaran kasar ta Crotia bata gasganta cewa ko Tomislav Salopek dan shekaru 30 da haihuwa mai yaya biyu, wanda kuma yake aiki a kasar ta Masar, lallai dimun-dimun shine aka kashe ba.
Idan haka tatabbata to shine mutum na farko da aka fille wa kai na wani dan kudanci da kungiyar Isil dake Masar wadda ta bayyana mubayiar ta ga kungiyar ta isil ta kame a yankin lardin Sinai.
Hoton da aka nuna a shafin twitter, ya nuna hoton wani mutum ne kwance kana wani tsaye bisan sa rike da wuka, kana ga tutar kungiyar mai launin baki daga gefe.
Bayanin dake kasar wannan hoton na cewa ne kungiyar ta dauki wannan matakin ne ne sakamakon yaki da kasar sa keyi da kungiyar ta isil.
Daya daga cikin bukatun yan taaddan a lokacin da suka kame shi Salopek shinre Cairo ta saki matan dake tsare a gidan yarin kasar su kuma har lokacin da suka bayar ya wuce abinda yasa suka sa, su daukar wannan matakin.
Sace wannan dan taliki ta haifar da tsoro ga kwararru masu aikin na musammam ga manya-mayan kanfanoni dake cikin kasar ta Masar