Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce har yanzu lokaci bai yi ba tukun, da za’a yanke hukuncin ko Kungiyar ISIS ce ta kai harin ranar Lahadi a jihar Texas ta kudu maso yammacin Amurka, inda wasu ke zanen barkwancin abin da su ka kira Annabi Muhammad (SAW).
Wannan Kungiya mai tsattsauran ra'ayin, ta yi ikirarin kai harin a gidan rediyonta jiya Talata. Ta ce biyu daga cikin askarawan Daularta ne, su ka kai hari a Garland kusa da Dallas. Ta ce wannan ne harinta na farko a Amurka, kuma wai kadanma aka gani.
Mai magana da yawun Fadar ta White Josh Earnest ya ce Gwamnatin Obama na kaffa-kaffa wajen shelar cewa 'yan ISIS sun shigo Amurka.
"Yace muna shakka saboda haka mu na bukatar karin sani game da gaskiyar lamarin. Akwai masu tsattsauran ra'ayi a fadin duniya, ciki har da masu alaka da ISIS, wadanda ke kokarin amfani da damar da kafafen sada zamunta kan bayar, su yi hulda da mutane a fadin duniya, ciki har da Amurka," a cewarsa.
'Yan sanda sun ce 'yan bindigar su ne Elton Simpson da Nadir Soofi. Mutane biyun sun bude wuta a harabar wurin taron, su ka raunata wani mai gadi kafin 'yan sanda su bindigesu har lahira.
Wasu takardun kotu na nuna cewa an jima ana sa-ido kan take-taken Simpson tun daga shekarar 2006, sannan kuma a shekarar 2010 hukumar bincike ta FBI, ta same shi da laifin shata mata karya, game da niyyarsa ta shiga kungiyar jihadi a Somaliya.
Wata kungiya ce mai suna American Freedom Defence Initiative, ta rajin kare 'yanci a Amurka, ta shirya gasar zanen barkwancin, inda ta yi tayin ladar dala 10,000 ga wanda ya fi kwarewa.