Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Yakin Amurka Zasu Fara Farma ISIS daga Turkiya


Barin wuta a birnin Homs na Siriya da jiragen sama suka haddasa
Barin wuta a birnin Homs na Siriya da jiragen sama suka haddasa

Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu, ya fada yau Laraba cewa jiragen yakin Amurka da ma wadanda basu da matuka sun fara isa wani sansanin mayakan sama a kudancin Turkiyya, gabannin kaddamar wani shiri na kawar da mayakan ISIS daga yankin Syria dab da gabar Turkiyyan.

Mr. Cavusoglu yace nan bada jumawa ba kasarsa da Amurka zasu fara gagarumin fada da 'yan kungiyar ISIS, da zai kai ga samar da yanayi da ya dace ga 'yan tawayen Syria masu sassaucin ra'ayi wadanda suke fafatawa da 'yan bindigar.

Ministan harkokin wajen yayi magana a lokacin ziyarar da yake yi a Malaysia, inda ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka John kerry a gefen taron kolin na yanki.

A cikin watan jiya ne Turkiyya ta amince da girke dakarun Amurka a wani sansanin mayakan samanta dake gari da ake kira Incirlik kusa da kan iyakarta da Syria daga kudancin kasar.

Jami'ai sun bayyana shirin a zaman wani kokari na kjirkiro da ani yankin da "babu 'yan ISIS", mai fadin kilomita 100 a arewacin Syria.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG