Yan kungiyar ISIS sun kara samun nasarar kame wasu yankunan dake wajen fadar gwamnatin kasar Iraqi, musamman wadanda ke yankin Anbar,kamar yadda mazauna yankin da wasu jamiaan gwamnati ke cewa.
Sun fara kai hari ne tun da yammacin jiya laraba, wasu dagacikin garuruwan da suka yi nasarar kamewa ko sun hada da wasu kauyuka 3 dake yankin lardin Ramadi.
Awannan yankin ne dai daruruwan sojojin Amurka dana hadin gwiwa ke horas da sojojin kasar ta Iraqi a Anbar,wanda yake yana da tazaran kilomita 110 daga yammacin Ramadi.
Shidai wannan wurin ya kasance karkashin isil din ne a tsakiyar watan fabarairu, domin ko suna kai hari hadi da na kunan bakin wake, wanda aka shawo kansa.
Sai dai Prime Minister Haider Al-Abadi ya fada a satin data wuce cewa sojojin Iraqi zasu mayar da hankali ne wajen kwato ikon lardin Anbar bayan sunyi nasarar kora kungiyar ta isil wajen birnin Tikrit.
A ciki farkon wannan satin ne dai Mr Abadi ya gana da shugaba Obama anan Washington domin neman Karin taimako akan yadda zasu fatattaki kungiyar ta isil.
Shugaba Obama yayi alkawarin basu dala miliyan 205 domin kasar ta gudanar da ayyukan jin kai amma bai furta cewa za a basu wani karin taimakon sojoji ba.
Kasar Amurka ce ke cikin sahun gaba wajen taimakawa kasar ta Iraqi yaki da kungiyar ta isil ta sama