Kungiyar ISIS ta kwace birnin Palmyra na kasar Syria, abinda ke haifar da fargaban wata sabuwar guguwar lalata kayan tarihin Musulmi masu daraja da ba za a iya maye gurbinsu ba.
Kungiyar kare hakin bil Adama ta kasar Syria mai cibiya a Birtaniya, tace dakarun Syria sun janye daga galibin wurare cikin birnin jiya Laraba da yamma bayan kazamin gumurzun da aka yi da mayakan a birnin dake arewacin kasar.
Palmyra yana da cibiyar kayan tarihin kungiyar UNESCO mai dumbi tarihi. Darektan cibiyar adana kayan tarihi na kasar Syria Maamoun Abdulkarin yace an kwashe daruruwan kayan tarihi daga birnin zuwa wadansu wurare dake da tsaro, sai dai akwai manyan kayan tarihi da ba za’a iya tumbukewa ba. Jami’an kasar Syria da na Majalisar Dinkin Duniya na kira ga kasashen duniya, su taimaka wajen kare wadannan wurare daga mayakan ISIS, wadanda suka lalata kayan tarihin dake kasar Iraq farkon wannan shekarar.