Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISIS: Kungiyar Ta Yi Bazanar Kai Hari Cikin Amurka


Sallar jana'izar mutane biyu da aka harbe da aka zargin 'yan kungiyar ISIS ne
Sallar jana'izar mutane biyu da aka harbe da aka zargin 'yan kungiyar ISIS ne

Kungiyar ISIS tace tana da sojoji 71 cikin jihohin Amurka 15 da zasu kai hari koyaushe suka samu umurnin yin hakan

Wata babbar barazana ta bullo daga wani ba’amarike da ake zargin ‘dan kungiyar ISIS ne, ta sa hukumar leken asiri ta Amurka kula, kodayake babu wasu alamu da ke nunin yiwuwar hakan.

An kafe barazanar ne a shafin yanar gizo da ake kira justpaste.it, sakon na cewa harin da aka kai na ranar Lahadi a garin Garland dake jihar Texas “somin tabi ne”

Sakon ya cigaba da cewa “muna da kwararrun sojoji 71 a jihohi 15, suna kuma jiran umarni daga garemu don kai hari duk inda muke so,”. Daga karshe mai rubuta sakon Abu Ibrahim Al Ameriki, wanda yake ba’amarike ne kuma ‘dan ta’adda da ake tsammanin yana can cikin wata kabilar Pakistan. Ya kuma rubuta cewa, “watanni shida masu zuwa zasu zamanto abin mamaki”

Al Ameriki wanda ya bayyana cewa Pam Geller, ‘daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar kare ‘yancin fadin albarkancin baki ta American, wato Freedom Defence Initiative, shi ne ainihin wanda aka auna a harin da aka kai a garin Garland. Wanda sune suka shirya taro a gurin da aka auna inda zasu yi gasar nuna zanen Annabi Muhammad (SAW).

‘Yan sanda dai sun gano ‘yan bindigar da suka kai hari Garland, kamar yadda suka bayyana sunayensu, wato Elton Simpson dan shekaru 31 da Nadir Soofi dan shekaru 34. Su biyun dai sun saka rigar kariya sun kuma raunata wani mai gadi bayan da suka bude wuta, amma ‘yan sanda dake gurin sun harbesu har lahira.

Mai magana da yawun fadar White House Josh Earnest ya fadi jiya Laraba cewa babu wata alama da take nunin cewa ko dai ‘daya daga cikin mutanen na aiki ne da umarnin kungiyar ta ISIL.

Jami’an hukumar leken asiri sun fada jiya Laraba cewa zasu ‘dauki sabon barazanar da Al Ameriki yayi da mahimmanci, amma sun kara da cewa tunda aka kafe wannan barana akan yanar gizo abin bai basu mamaki ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG