Mayakan kungiyar nan mai da'awar kafa daular Islama (ISIS), sun tuka wata mota shake da bama-bamai zuwa wani sansanin 'yan sandan Iraki a jiya Litini, su ka hallaka mutane akalla 37 tare da raunata wasu da dama, a cewar jami'an tsaron Iraki.
Harin kunar bakin waken, wanda aka kai Samara, arewa maso gabashin birnin Bagadaza kuma arewa da birnin Ramadi da ke hannun ISIS, an auna shi ne kan jami'an tsaro, kuma ya janyo tarwatsewar wani wurin ajiyar makamai.
Sojoji da sauran mayaka na amfani da sansanin ne a matsayin wurin shirya hare-hare kan mayakan ISIS.
Sojojin gamayyar da Amurka ke jagoranta, sun cigaba da kai hare-haren jiragen sama cikin dare har, sau 13 a Syria yawanci akan Hassakeh.