Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

IRAQ: Mayakan ISIS Sun Kutsa Cikin Matatar Man Fetur Dake Bayji


Wadanda mayakan ISIS suka tilastawa barin muhallansu a Iraqi
Wadanda mayakan ISIS suka tilastawa barin muhallansu a Iraqi

Ma'aikatan Tsaron Amurka ta tabbatar cewa mayakan ISIS sun kutsa cikin matatar man fetur din Bayji wacce ta dadae bata aiki.

Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon tace mayakan ISIL dake kasar Iraqi, sun kutsa cikin matatar man fetur ta Bayji da ake ta kaddama akai.

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron ta Amurka Kanal Steve Warren yace cikin sa’o’oi48 da suka wuce ne mayakan sakan suka kutsa cikin matatar.

Ya cigaba da cewa jami’an tsaron kasar Iraqi suna cikin harabar matatar man, kumaa halin yanzusun hana mayakan kamamatatar man. Amurka da sauran sojojin hadin gwiwa sun kai hare haren jiragen sama a kalla biyar a kewayenmatatar man, cikin sa’o’i 24 da suka wuce a yunkurin fatattakar mayakan sakan.

Garin Bayji dai na kan hanyar zuwa birnin Mosul wanda yake birni mafi girma da mayakan sakan suka kwace. Warren dai yace yankin da matatar man fetur ‘din take shine muhimmanci. Matatar ta dade bata aiki.

XS
SM
MD
LG