Bayan sanarwar shugaban hukumar zaben yace za'a cigaba da karbar takardun 'yan takara har zuwa ranar 24 na watan Oktoban wannan shekarar kafin a bude yakin neman zabe a ranar 29 na watan Oktoba din.
Jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulkin kasar ta bakin sakataren watsa labaranta na birnin Tawa, Muhammad Abdulkadir ta bayyana gamsuwa da jadawalin saboda lokacin an kare ayyukan gona kowa zai samu ya kada kuri'a.
Amma mai magana da yawun jam'iyyar MNSD Nasara ta 'yan adawa, Rabilu Alhaji Kani ya nuna shakku dangane da shirin hukumar zaben wadda yace ta nuna gazawa a zabukan da suka gabata. Yace mutanen CENI ba gaskiya suke so ba saboda haka ba zasu yi zaben gaskiya ba. Yace da gwamnati da CENI uwarsu daya ubansu daya yana cewa doka bata ba CENI daukan matakin da ta dauka ba.
A can baya dai sau biyu hukumomin kolin kasar Nijar tare da izinin majalisar dokokin kasa ke karawa kansilolin kasar wa'adi saboda dalilan gudanar da sahihin zabe, matakin da 'yan siyasar kasar suka yi na'am dashi yayinda masu rajin kare dimokradiya ke nuna rashin gamsuwarsu saboda wai alama ce ta rashin ba kananan hukumomi mahimmanci.
Ga karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5