Wadannan kungiyoyin fafutuka da ake kira Resistance Citoyen, sun bayyana cewa wani taron nazarin da sukayi akan yadda al’amuran mulki ke gudana a kasar ta Nijar a yau, shine ya basu damar gano alamomi masu karfi na shirin shimfidar da mulkin kama karya a kasar da talakawanta suka rungumi tafarkin dimokaradiyya shekaru fiye da 25.
Hakan yasa suka kudiri aniyar yakar wannan sabon salon mulki. Shugaban kungiyar matasan NIjar ta MOJEN, Surajo Isa, wanda ke zama daya daga cikin jagora a wannan yunkuri, yace wannan ba zargi bane abune wanda ya tabbata a cikin kasar Nijar.
To sai dai shugaban kawancen kungiyoyi na ROZEN Abdu Mamman Lokoko, mai ra’ayin gwamnatin Isuhu Mahamadu, na kallon korafin na takororin na sa na Resistance Citoyen a matsayin maras digi. Inda yace mutanen Nijar ne suka zabi shugabansu, wanda hakan ya bashi damar mulkar kasar.
Kawancen na Resistance Citoyen, ya yanke shawarar shirya jerin gwano da taron gangami a ranar 24 ga wannan wata, don nuna rashin amincewa da salon tafiyar ta gwamnatin Nijar.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan.