Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cuwa-Cuwa A Jarabawar Daukar Ma’aikata a Janhuriya Nijar


Shugaba Mahammadou Issouffou
Shugaba Mahammadou Issouffou

Ga dukkan alamu Shugaba Issouffou Mahammadou ya fara tauna tsakuwa dangane da masu cin hanci da rashawa a kasar. Mai yiwuwa ya gadar da kasa marar cin hanci kamar yadda ya yi alkawari

Kungiyar yaki da almundahana ta “Transparency International” shiyyar janhuriyar Nijar ta aika ma Shugaba Issouffou Muhammadou takardar bukatar ya gaggauta kawo karshen cin hanci da rashawa a jarabawar daukar ma’aikatan gwamnatin kasar.

Babban Sakataren INLC a kungiyar ta “Transparency International,” Malam Inwa Wada ya gaya ma wakilinmu a Niamey Souley Barma cewa bayan da Shugaba Issouffou Muhammadu ya samu wasikar tasu sai ya kira su ya basu tabbacin cewa zai gadar da kasa marar matsalar cin hanci da rashawa a karshen wa’adinsa.

Souley Barma ya kuma bayyana cewa Shugaban kasar ta Nijar ya umurci hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta binciki wannan zargin don daukar matakin da ya dace. Hasalima Barman ya ruwaito Mataimakin Shugaban Hukumar, Malam Salisu Uban Doman a cewa samun wasikar da Shugaba Issouffou Muhammadou ke da wuya.

Ga Souley Mummuni Barma da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG