Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin fararen hula na Nijar na shirin zanga zanga kan salon mulkin kasar


Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar da kungiyoyin ke zargin yana shirya aiwatar da mulkin kama karya
Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar da kungiyoyin ke zargin yana shirya aiwatar da mulkin kama karya

Jiya Lahadi kungiyoyin suka shirya zasu yi gangami domin nuna damuwarsu akan abun da suka kira take-taken gwamnatin kasar Nijar na aiwatar da mulkin kama karya amma hukumomi suka hanasu bisa dalilin cewa basu da isassun jami,an tsaro

Bisa ga wasikar da mahukumtan birnin Yamai suka rubutawa kawancen kungiyoyin ya sa suka dage taron gangamin da suka shirya yi jiya Lahadi a brnin.

Tuni kungiyoyin suka shirya bullo da wani salon na daban. Musa Sangari daya daga cikin jagororin kungiyoyin yace hanasu yin zanga zanga nuni ne cewa suna da gaskiya bisa ga zargin da suke yiwa gwamnatin na son kafa mulkin kama karya. Yace dole zasu fito su yi gwagwarmaya domin idan basu yi ba gwamnati mai ci yanzu zata jefa kasar cikin mulkin kama karya.

Shugabannin sun kira duk mutanensu su zauna gidajensu ranar Alhamis Afirilu 28, 2016. Dangane da zanga zangar da suka shirya suka ce zasu yi ranar Asabar mai zuwa, wato Afirilu 30, 2016.

A zantawa da ya yi da Muryar Amurka shugaban hadin kungiyoyin dake goyon bayan gwamnatin shugaba Mahammadou Issoufou, Abdu Mamman Lukoko ya bayyana cewa dimokradiyar Nijar na nan daram. Yace dimokradiya ce ta sa a ka bar kungiyoyin adawa suna fadin abubuwan da suke fadi. Yace wani wuri ko mutum na son fadin magana ba zai yi ba domin ya san inda za'a ajiyeshi. Yadda 'yan adawan suka shiga kafofin labarai suna bayyana ra'ayoyinsu abu ne da dokar kasa ta tanada. Taba kowa 'yancin ya fadi albarkacin bakinsa a karkashin mulkin dimokradiya.

Lukoko yace su ba zasu shiga zanga zangar ba domin bujirewa doka ne. Ba zasu goyi bayan karya dokar kasa ba. Idan ana karya doka to babu dimokradiya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG