A rahoton na Arlit da ta mikawa shugaban gundumar Arlit din jami'an tsaro sun sa ido akan wasu mutane dari da hamsin da uku wadanda saura kadan a tsallaka dasu zuwa kasar Algeria.
Mutanen sun hada da maza goma sha biyar da mata arba'in da shida da yara tasa'in da biyu.An mayarda mutanen garin Agades.
Shugaban Arlit ya yiwa manema labarai karin haske akan lamarin. Yace akwai wasu ma da suka rasa rayukansu an jefar da gawarwakinsu kan iyaka. Amma saboda Allah ya sa mutanen da aka kama suna da sauran shan ruwa ya sa jami'an tsaro suka ganosu. Yace ko a cikin gari sun kama mutane tamanin da uku manya da yara. Sun mayarda yaran ga iyayensu.
Wadannan 153 da aka kama nuni ne yadda masu safarar mutane ke bata sunan Nijar. Yace dalili ke nan mahukumta suka tashi tsaye su kawar da matsalar. Sabili da zaben kasar suka maida hankali kan jama'ar kasar domin tabbatar da zaman lafiya. Yanzu an kammala zabe saboda haka mahukumta sun dawo kan kula da iyaka gadan gadan.
Ga karin bayani.