Sun kuma tattauna matsalolin dake kawo kwararar matasa zuwa Turai ta barauniyar hanya.
Daga bisani ministocin harkokin wajen kasashen uku suka kira taron manema labarai na hadin gwuiwa.
Ministan harkokin wajen Nijar Ibrahim Yakubu yace sun yi lissafi kowace shekara mutane sun kai dubu dari dake ratsawa cikin Nijar domin su tsallaka zuwa Turai. Yace sun fada masu cewa idan har mutum ya bar kasarsa to akwai matsala. Ba banza kawai zai bar kasarsa ba. Akwai talauci. Akwai yunwa. Akwai kuma rashin kwanciyar hankali.
Idan ana son a magance matsalar to sai su taimakawa kasar Nijar wadda take bukatar kudi miliyan 660 na sefa.
Ministan yace yanzu ma sun taimaka da kudin Euro miliyan 75 a kokarin rage matsalolin.
Akan yaki da ta'adanci yace kodayake karfin Boko Haram ya ragu amma har yanzu yakin na nan. Saboda haka yakamata a tsaya daram a cigaba da yakin.
Har yanzu ana haifar ta'adanci a Mali kana a yadashi yankin kasashen Sahel.
Ga karin bayani.