Onarebul Iro Sani mataimaki na farko na kakakin majalisar dokokin kasar yace dokokin biyu da suka amince dasu sun shafi ayyukan wutar lantarki da za'a yi a garuruwa dari biyu da goma sha daya.
Cikin garuruwan dari biyu da goma sha daya akwai wasu yankuna hamsin da biyar da suma zasu samu wuta daga garuruwan.
Kodayake 'yan adawa sun amince da shirin amma suna cewa ba girin-girin ba ta yi mai. Kakakin gungun 'yan majalisa masu adawa Onarebul Lamido Mummuni Haruna yace an bada shekaru biyu a maida kudin.Burinsu ne a ciwo bashi wuraren da za'a samu da sauki ba tare da wasu sharudda ba. Yace sun yadda a ciwo bashi a yiwa talakawa aiki amma ba wasu su wawure kudin ba aikin kuma ba'a yi ba.
Wani abu kuma da 'yan adawa suka nuna damuwa kai shi ne rashin saka yankin Diffa a tsarin. Yace Diffa tana cikin matsala bai kamata a cireta daga shirin ba.Yanzu ne Diffa ke bukatar wuta.
Amma a bangaren masu rinjaye lamarin ba haka yake ba. Sun ce akwai shiri na musamman da suka yiwa Diffa saboda garuruwan Diffa nada nisa. Yace sun sani tana cikin uzuri saboda haka shiri na daban za'a yi mata.
Ga karin bayani.