Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Nijar ta samu koma baya kan kare 'yancin 'yan jarida


Shugaban Nijar Issoufou Muhammadou
Shugaban Nijar Issoufou Muhammadou

Rahoton kungiyar dake auna 'yancin 'yan jarida da damar fadin albarkacin baki kowace shekara dake kasashen turai ya ayyana Nijar a matsayin kasa ta hamsin da biyu a shekarar 2015 a duniya maimakon ta arba'in da bakwai da take a shekarar 2014

Rahoton da aka fitar kan aikin jarida a Nijar na shekarar 2015 ya nuna kasar ta samu koma baya da maki biyar wajen kare 'yancin 'yan jarida da aikin jarida da kuma damar fadin albarkacin baki ba tare da tsangwama ba daga mahukumta.

'Yancin 'yan jarida da 'yancin aikin jarida da damar fadan albarkacin baki cikin walwala nada mahimmanci a gina dimokradiya.

Tuni kungiyoyin kare hakkin 'yan jarida suka fara bayyana dalilan da suka sa aka samu koma baya. Malam Bubakar Gyallo na cikin shugabannin kungiyoyin kuma yace masu mulki da suke rike da iko basa aiki da dokokin kare hakkin 'yan jarida. Duk da cewa doka ta hana amma ana kama 'yan jarida ana kullesu. Yace yanzu neman labari ma ya zama laifi maimakon a bari ka samu labari ka wallafa idan kuma ba gaskiya ba ne sai a waiwayi dan jaridan da ya wallafashi.

To amma hukumomin Nijar na alfaharin kare 'yancin 'yan jarida da samun damar fadin albarkacin baki. Ko a baya bayan nan shugaban kasar Issoufou Mahammadou ya bugi kirji da cewa a karkashin mulkinsa 'yan jarida sun samu 'yanci lokacin da yake rantsuwar kama mulki wa'adi na biyu a ranar Afirilu 2, 2016. Yace a tsawon shekaru biyar na mulkinsa Nijar ta samu 'yancin aikin 'yan jarida lamarin da ya sa ta zama kasa ta 47 a duniya ko ta 7 a Afirka a shekarar 2014.

Abubakar Gyallo yace idan aka yi la'akari da abun dake faruwa a zahiri ikirarin shugaban kasar ya yi kama da batun siyasa. Yace farfaganda ce shugaban ke yi. Mutane suna gani a fili abubuwan dake faruwa. Nijar bata cika alkawari kuma bata kare 'yancin 'yan jarida.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG