To amma al'ummomin jihar ta Adamawa daya daga cikin jihohin da rikicin Boko Haram ya daidaita sun fito fili suna bayyana ra'ayoyinsu dangane da sauyin da shugaban kasa ya yi.
Wasu suka ce sabon shugaban Najeriya ya san tafiyar hafsoshin ba ta gari ba ce dole ne ya canzasu.Ganin yadda jami'an tsaro da ma'aikata ke zuwa aiki da wuri wani yace dole ne domin an samu canji.
Wani Isa Zailani yace canjin da shugaban kasa yayi ya yadda dashi. Yadda sojoji ke fita zuwa tunkarar 'yan ta'ada ya san lallai yanzu da gaske ake yi da yakar 'yan ta'adan.
Yusuf Usman Gire yace gaskiya yakamata sabbin shugabannin da aka nada abun da ya faru ya zama masu daratsi, wato su yi koyi da kurakuran da na baya suka yi. Su rike mukamansu da gaskiya. Su yi aiki tsakaninsu da Allah kamar yadda shi shugaban kasa Buhari ya nuna gaskiya a yadda ya zabosu..Ya basu amana su ma su rike amanar jama'a.
Janar Saleh Maina mai ritaya ya kira shugaban kasa ya ba sabbin hafsoshin wa'adin kammala aikin kakkabe 'yan Boko Haram domin ba'a yi haka ba can baya shi ya sa suka yi sakaci.
Akwai wasu kuma da suka ce sabuwar gwamnati ta duba batun sojojin da aka kora ko aka yiwa hukunci saboda rikicin Boko Haram. Suna cewa akwai wadanda ba'a yi masu adalci ba. A duba a kuma dawo dasu idan har ana son a tabbatar da adalci.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5