Manazarta na ganin dole mahukuntan kasar Najeriya su tashi tsaye soboda shawo kan wannan matsala da take son ta zama tamkar kayar kifi a makokwaro.
Na baya bayn nan shi sace wani hamshakin wani dan kasuwa da aka yi a Mararrabarbaisa dake cikin jihar Taraba. Sai da 'yanuwansa suka biya makudan kudade kafin a sakoshi da safiyar ranar yau.
Wanda aka sacen bai iya magana da Muryar Amurka ba saboda firgita to amma wani makwafcinsa da ya nemi a sakaya masa suna ya yi karin bayani.
Makwafcin yace an biya kudin fansa kafin a sakoshi. Yace to amma lamarin abu ne wanda ba za'a so a yi bayani ba. Mutanen garin suna zaman dar dar domin irin hakan bai taba faruwa a garin ba. Yanzu 'yan garin basu yadda da kokwane bako ba.
Yace sun biya kudin fansa domin wani lokacin idan aka yi kokarin yin anfani da jami'an tsaro za'a yi asarar rai. Dalili ke nan da iyalan suka yanke shawarar biyan kudin fansa.
Saboda matsalar sace mutane na yaduwa ya sa wasu kungiyoyi sun tashi haikan su yi taimako kamar kungiyar Fulani da yanzu take taimakawa. Alhaji Aliyu Nuhu sakataren kungiyar Fulanin yace suna aiki hanu da hanu da hukuma. Sun kama wasu masu sace mutane da shanu a jihar Adamawa kuma sun mikasu ga jami'an tsaro.
Jama'a na biyan kudin fansa ne saboda gudun kada a kashe 'yanuwansu domin wadanda suke sace mutane idan ba'a biyasu ba suna kashe mutane.
Ga karin bayani a rahoton Ibrahim Abdulaziz.