“Me zan fadawa shugaban kasar mu yanzu? Na farko dai, ka san mu Musulmai ne da Christians. Saboda haka kayi wa shugaban ka addu’a, Allah Ya ba shi nasara.
Misalin watanni 11 kennan da tsige Murtala Nyako daga kujerar gwamna a Jihar Adamawa. Nyako na da sako ga mutan Adamawa akan dalilan da suka sa ya bar Najeriya.
“Dalilin da yasa na bar Najeriya, ka yi musu tuni. Annabi Musa yayi hijira. Annabi Isa yayi hijira. Annabi Muhammadu (S.A.W) yayi hijira. Na tabbata musu ba karya nake ba, sau biyu aka so a kashe ni. Ana so a kashe ka, sai ka zauna kana wawanci?” inji Nyako.
Sai dai Hukumar Kula da Cin Hanci ta EFCC ta tsare Murtala Nyako bayan dawowarsa Najeriya.
“Litattafai da akayi ta yi akaina suna da yawa. Sunce in je, sai naje nace gani. Kayi tambayanka, kuma ka kawo mini shaida wanda ni nayi magudi a zama na, na Adamawa. In ka samu kudina a kasar waje, ka kaini gidan fursuna” inji tsohon gwamnan.
Murtala Nyako wanda tsohon babban hafsin sojin ruwa ne ya shiga takun saka da tsohon shugaba Jonathan a lokacin da ya zarge shi da hannu a kashe-kashen Boko Haram. Jim kadan ‘yan majalisa suke tumbuke Nyako daga kujerarshi ta gwamnan jihar Adamawa, sannan yayi balaguro zuwa kasar waje.
Kasa da mako daya da rantsar da sabon shugaba Muhammadu Buhari, Nyako ya dawo Najeriya.