Sarakunan sun sake jaddada mahimmancin zaman lafiya a wannan lokaci mai albarka tsakanin musulmai da ma wadanda ba musulmai ba musamman ganin irin halin da arewa maso gabashin kasar Najeriya ta samu kanta a ciki.
Sun jawo hankalin jama'a akan irin bala'in da 'yan Boko Haram suka jefa yankin ciki na shekaru da dama. An yi asarar rayuka da dimbin dukiyoyi. Dubban jama'a kuma aka rabasu da jidajensu. Wasu har yanzu suna kan komawa kauyukansu da gidajensu.
Mai martaba sarkin Ganye Ganwari na biyu Alhaji Umaru Adamu Sanda ya shawarci al'ummar musulmi da su yi anfani da watan azumi wajen yiwa shugabanni addu'a musamman a wannan lokacin da 'yan Najeriya suke zuba ido su ga kamun ludayin sabuwar gwamnatin Buhari da zummar zata kawo masu canji.
Sarkin ya kira jama'a su lura da kalmomin dake fitowa daga bakunansu. Yace su yi maganar da zata hada kawunan musulmai da wadanda ba musulmai ba. Su yi anfani da lokacin azumi su rokawa kasar da shugabanninta domin su samu su warware matsalolin da suka addabi jama'a.
Shi ma sarkin Mubi Mai Martaba Alhaji Abubakar Isa Ahmadu wanda kungiyar Boko Haram ta daidaita ya gargadi duk musulmai da su gyara halayensu, su yawaita yin ibada da kuma zuwa kusa da Ubangiji domin gujewa sake fadawa cikin wata masifa. Yace kamata yayi bala'in da ya fadawa yankinsa ya zama daratsi garesu. Sarkin ya bukaci musulmi da su yiwa kasar da duniya gaba daya addu'ar neman zaman lafiya.
Ga rahoton Sanusi Adamu.