Shedun gani da ido sun tabbatar da faruwar lamarin fashewar inda suka shaidawa wakilin Muryar Amurka cewa ya farune a wani guri da ‘yan Babura ke taruwa.
Fashewar bom din ya auna mutane dayawa wanda dayawa daga cikin bazasu iya tafiya ba, amma a kwai asarar rayuka dayawa da baza’a iya fadi ba a halin yanzu kasancewar mutane na ta gudu alokacin da abin ya faru.
Kawo yanzu dai jami’an tsaro sun killace gurin da abin ya faru, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa DSP Usman Abubakar ya tabbatar da faruwar fashewar bom din kuma yace basu da yawan alkaluman mutanen da suka rasa rayukan su.
Wannan dai shine karo na farko da bom ya fashe a jihar Adamawa tun rantsar da sabuwar gwamnati, duk da yake babu wata kungiya da ta fito ta ‘dauki alhakin kai wannan hari.