Dr. Bala Sai'd, wanda shine babban Likita a babban asibitin jinya ta tarayya dake Yola, yayi kira na neman tallafi tako wani fanni daga kayan aiki zuwa jini.
Babban likitan yayi wannan kiran ne lokacinda tawagar wakilan uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, wacce uwargidan tsohon Gwamnan jihar Hajiya Zainab Murtala Nyako ta wakilta, tace uwargidan shugaban kasar, tana jajantawa wadanda harin ya rutsa dasu, tareda bada gudamawa da ba'a bayyana yawansa ba.
Sai dai dangin wadanda harin ya rutsa da su sun koka kan karancin kayan jinya, kuma su da kansu suke dawainiyar 'yan uwansu da suka jikkata.
Babban likitan Bala Sa'idu, yace kungiyoyi kamar su Red Cross, da mai martaba Lamidon Adamawa Dr. MUhammadu Barkindo Aliyu Mustapha, da wasu daidaikun mutane sun bada gudamawa.
Shugaban 'yan Kasuwa a yankin, Ibrahim 86' yace, zuwa yanzu dai 'yan kasuwa maza da mata 35 ne suka tantance sun halaka sakamakon harin da aka kai a ksuwar Jimetan.