Rahotanni daga birnin Yola a Jahar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa yawan mutanen da suka mutu a harin bam din da aka kai a kusa da kasuwar Jimeta na ci gaba da karuwa.
Wakilin Muryar Amurka ya ruwaito cewa fiye da mutane 31 ne yanzu haka aka tabbatar da mutuwarsu a wannan hari da aka kai.
“Muna da mutane 31 wadanda Allah ya musu cikawa, wadanda suka jikkata muna da mutane 38 a asibiti, kuma wasu suna cikin mawuyacin hali, wasu kuma har an sallame su daga asibitin.” Inji Alhaji Sa’adu Bello, wani jami’in hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA a Yola.
Ya kuma kara da cewa ana bukatar jini domin an samu karancin sa a dakin adana jinin asibitocin.
“Muna rokon mutane su yi kokari su je asibitocin nan guda biyu su ba da na su gudunmawa domin a samu sauki wajen jinyar wadanda suka jikkata.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jahar ta Adamawa DSP Usman Abubakar ya ce cikin wadanda suka rasa rayukansu har da ‘yan kunar bakin waken.
“A dinga kula da wadanda su ke kai kawo, duk mutumin da ba ka yarda da shi ba, ka yi kokarin ka sanar da jami’an tsaro.” Inji DSP Abubakar.
Ga karin bayani a rahoton Ibrahim Abdulaziz: