Mutane na korafin cewa rashin kammala aikin gina madatsar ruwan Chouci ya jawo masu babbar illa. Yanzu tamkar murnarsu ta koma ciki ne.
Masu aikin, da aikin yanzu duk babu su. Jama'ar wurin na fatan sabuwar gwamnatin shugaba Buhari zata kammala aikin idan ma aka yi la'akari da cewa lokacin da shi shugaban kasa yake shugabancin asusun rarar kudin man fetur ko PTF ya fara ginata.
Kawo yanzu dai an kashe makudan kudi ba tare da cimma nasarar kammalata ba kamar yadda manoman wurin suka shaida. Manoma wurin sun koka da shakulatin bangarancin da suka ce ana nunawa game da madatsar ruwan.
Ita dai madatsar an fara ginata ne tun lokacin hukumar PTF da shugaban kasa na yanzu ya jagoranta. An kashe fiye da nera biliyan biyar ba tare da aikin ya je koina ba. Aikin madatsar na cikin manyan ayyukan da hukumar PTF ta dankawa gwamnatin Obasanjo a shekarar 1999. Tun a lokacin ne ake ta fitar da makudan kudade da zummaR aiwatar da aikin amma babu inda aikin ya je fiye da shekaru 17.
Manufar aikin shi ne a inganta aikin noma, samar da abinci, da kuma rage ambaliyan ruwan da ake fama dashi a yankin da ma jihar gaba daya. Aikin madatsar idan an kammala zai samar ma manoma zarafin rungumar noman rani.
Masana ma sun koka da yadda aikin ke tafiyar hawainiya cikin shekaru 17 da aka kwashe ana aikin..Mr. Joseph Jarium wani masani akan harkokin noma yana ganin muddin aka kammala aikin dubban jama' ne zasu samu aikin yi. Yace za'a samu manoma kamar dubu talatin da zasu yi aiki a wurin. Idan ba'a gama aikin ba bana abinci zai yi wuya.
Sanata Abdulaziz Murtala Nyako dan majalisar dattawa dake wakiltar yankin Adamawa ta tsakiya inda madatsar ruwan Choucin take yace ya tabbata shugaban kasa na yanzu zai taimaka a gama musamman tunda shi ne ya fara aikin.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.